Tsohon Kwamishinan Kudi na jihar Kano, Farfesa Kabiru Isa Dandago ya zargi gwamnatin tarayya da bullo da harajin gado cikin kudirin dokar haraji da ake takaddama a kai.
Kudurin dake gaban majalisar dattawa yanzu haka na cigaba da shan suka daga manyan Arewa bayan yi masa karatu na biyu, sai dai kafin yanzu babu wani masani da ya gano batun harajin gadon da Farfesa Dandago yace an boye shi cikin dokar.
Farfesan ya shaidawa DAILY POST HAUSA cewa babi na biyu sashi na daga, saki layi na uku, yayi bayani kan kudin iyali da za a cire gado a ciki kafin a raba.
“Wannan ba shine karon farko da aka taba bijiro da harajin gado ba a Najeriya, tsohon sbugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gwada yin haka a 1979 sai dai marigayi Janar Sani Abacha ya soke dokar lokacin mulkinsa bayan malaman addinin muslunci da na kirista sun kalubalance ta” .
Sidarar ta tanadi cire haraji cikin kudin gadon da Iyali zasu samu kafin a raba, sai dai bata fayyace ko nawa ne za a cire ba, amma Farfesa…