‘Yan bindiga sun sace amarya da kawayenta no moo to hudu a karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sakkwato.
Harin ya faru ne a ranar Asabar a kauyen Kwaren Gamba, kusa da Kuka Teke, wuri da aka saba kai hari daga kungiyoyin ‘yan bindiga da ke da alaka da Bello Turji.
Ganau sun bayyana cewa maharan sun dira yankin tare da sace mutanen, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali.
Wani masanin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa al’ummar yankin suna cikin tsananin dimuwa.
Iyayen wadanda aka sace suna cikin halin bakin ciki, inda wani dattijo a kauhen ya ce, “Halinda muke ciki ya fi karfin mu, kuma mutanenmu suna rasa kwarin guiwa.”
A kwanakin baya, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 10 a Jihar Sakkwato.
‘Yan bindiga sun kai hari a kauyen Dantudu Lajinge, inda suka kashe ‘yan sa-kai tara tare da sace matan su.
Wani mazaunin kauyen, Bello Dan-Tudu, ya ce, “Sun yanka mutane tara kamar awaki.”
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa…
Connect with us on our socials: